Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

- Sojoji da yan sakai na maharba sun dakile wani yunkuri kai hari da wasu ‘yan Boko Haram suka yi yunkurin yi

- ‘Yan bindiga masu tada kayar bayan na kokarin sake kai mummunan farmaki ne, to amma kuma basu taki sa’a ba

Rahotanni daga yankin Madagali a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa sojoji da yan sakai na maharba sun dakile wani yunkuri kai hari da wasu ‘yan Boko Haram suka yi yunkurin yi.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da al’ummomin yankin ke ci gaba da gudanar da bukukuwan samun zaman lafiya, biyo bayan kwato yankin daga hannun mayakan Boko Haram.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto daga yankin na Madagali an bayyana cewa ‘yan bindiga masu tada kayar bayan na kokarin sake kai mummunan farmaki ne, to amma kuma basu taki sa’a ba, inda sojoji da kuma yan sakai na maharba suka yi musu kofar rago.

Jami’an tsaro sun dakile harin da yan Boko Haram suka kai a Adamawa

Shugaban masu aikin sa kai, Adamu Abdullahi

Wani dan sakai na maharba yace sun yi yunkurin kai harin ne a gefen Waga Chakawa dake kusa da dajin Sambisa, inda yace an kashe mayakan Boko Haram da dama.

KU KARANTA KUMA: Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Shima kwamandan yan sintiri na yan banga a jihar Adamawa, Adamu Abdullahi ya tabbatar da faruwan lamari da ma irin nasarar da aka samu akan yan kungiyar ta Boko Haram.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umman ta Madagali ke bukukuwan murnar samun zaman lafiya. To ko yaya al’umman yankin suka ji da wannan yunkuri na Boko Haram. Yusuf Mohammad, dake zama shugaban karamar hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana hadin kan da ake samu a yanzu.

Madagali dai itace karamar hukumar farko da mayakan Boko Haram suka fara kwacewa a jihar Adamawa, inda suka ci karensu babu babbaka kafin daga bisani dakarun Najeriya suka kwato yankin, wanda kuma kawo yanzu akan dan samu harin sari ka noke a wasu lokutan, batun da dan majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da Michika Mista Adamu Kamale, ya yi kira da a kara sansanonin soji a yankin.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon yadda za'a murkushe yan ta'addan Boko Haram.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel