Yadda Masarautar Kano ta shiga cikin matsala

Yadda Masarautar Kano ta shiga cikin matsala

– An fara binciken Masarautar Kasar Kano

– Ana zargin Masarautar da barnatar da makudan kudi

– Dama akwai kishin-kishin din nema a tsige Sarki Sanusi II

Yadda Masarautar Kano ta shiga cikin matsala

Barna da dukiya: An fara binciken fadar Kano

Kwanan NAIJ.com ta fara samun jita-jitar cewa wasu Gwamnonin Arewa na kokarin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II inda har aka ce wasu daga cikin Gwamnonin sun yi wani taro game da Sarkin a kasar China.

A kwanan baya ne dai wani Marubuci kuma Dan Jarida mai suna Ja’afar Ja’afar yayi wani rubutu har kashi biyu inda ya bayyana irin makukun kudin da fadar Kano ta rika batarwa wajen sayen manyan motoci da kuma kudi na hawa shafin yanar gizo.

KU KARANTA: An fara binciken fadar Kano

Yadda Masarautar Kano ta shiga cikin matsala

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Yanzu dai Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa an fara binciken fadar saboda korafi da Jama’a su ka rika kai wa. Tuni dai har an nemi Ma’aji da Sakataren Masarautar domin su yi bayanin yadda aka kashe kusan Naira Biliyan 4 cikin ‘yan watanni kadan.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Muhammad Garba dai ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje bai da hannu wajen binciken. A wata rana dai sai fadar ta tura sama da Naira miliyan 100 ta asusun banki inji majiyar wanda yayi matukar yawa.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka ki sakin Dasuki

Yadda Masarautar Kano ta shiga cikin matsala

Sarkin Kano ya shiga cikin matsala

Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali ya tabbatar da cewa sun karbi takarda daga Jami’an ‘Yan Sanda da Hukuma inda ake bukatar su bayyana zuwa Ranar 3 ga watan Mayu domin yi wa Hukuma bayani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Fasto ya koma addinin Musulunci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel