Abin da ya sa Buhari bai hukunta Babachir tun farko ba

Abin da ya sa Buhari bai hukunta Babachir tun farko ba

- Ministan shari'a ya ce rashin gamsuwa da shaidar ha'incin da ake tuhumar sakataren gwamnatin tarayya, David Lawal Babachir ne ya sa shugaba Buhari bai dauki mataki a kansa ba

- A makon da ya gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Babachir Lawan

- Shugaba Buhari ya kafa kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo domin bincika zarge-zargen

Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce rashin gamsuwa da shaidar ha'incin da ake tuhumar sakataren gwamnatin kasar, David Lawal Babachir ne ya sa shugaba Buhari bai dauki mataki a kansa ba.

A makon da ya gabata ne dai NAIJ.com ta kawo rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Babachir Lawan da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar, Ayodele Oke, bisa zarge-zargen sabawa dokokin aiki da aikata cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Shugaban ya kuma kafa kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo domin bincika zarge-zargen, lamarin da wasu suke ganin akwai lauje a cikin nadi.

Abin da ya sa Buhari bai hukunta Babachir tun farko ba

Babban sakataren gwamnatin tarayya da aka dakatar

A baya, kafin wannan kwamiti dai shugaban ya kafa kwamiti karkashin jagorancin ministan shari'a Abubakar Malami kan batun zargin da ake yi wa Mista Babachir Lawal.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon da aka maka tsohon shugaban NNPC, Andrew Yakubu a Kotu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel