Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

– Shugaban Hukumar EFCC ya bayyana adadin kudin da Hukumar sa ta gano bana

– Ibrahim Magu yace EFCC ta samu Naira Biliyan 17 cikin ‘yan watanni

– Magu yace babu gudu babu ja da baya

Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Magu yace babu gudu babu ja da baya

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bayyana cewa Hukumar sa ta bankado sama da Naira Biliyan 17 daga cikin watanni 4. Ibrahim Magu ya kara shan alwashin cewa sai ya ga bayan satar dukiyar Jama’a a Najeriya.

Sabon tsarin nan da aka kawo na tona-ka-samu-rabon ka ya taimaka ainun wajen gano kudin da aka sace a kasar nan. A dalilin hakan an samu N521, 815, 000.000 da kuma $53,272,747.000, da kuma £122.890.00 da €547,730.00.

KU KARANTA: An gano laifin Sambo Dasuki

Ka ji adadin kudin da Ibrahim Magu ya bankado a wannan shekarar

Ibrahim Magu ya bankado makukun kudi bana

Mr. Ibrahim Magu ya bayyana wannan ne a wani taro da aka yi a Abuja Ranar Asabar dinnan. Inda ya kara da cewa sun gurfanar da mutane 62 a Kotu wanda tuni aka maka su a gidan yari a shekarar bana.

Makon jiya mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya gana da shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu na dogon lokaci ana masa tambayoyi. Osinbajo dai aka nada shugaban kwamiti da za ta binciki tsohon Sakataren Gwamnatin Mr. Babachir David Lawal.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An maka shugaban EFCC na da a Kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel