ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

- Manyan ofishosin hukumar sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram bayan sun gano bama-bamai da mayakan Boko Haram sun binne a karkashin kasa

- Lamarin ya faru a jiya, Asabar, 22 ga watan Afrilu yayinda suka tafi garin Gwoza daga garin Bama

Mukaddashin mai magana da yawun hukumar sojojin Najeriya mai suna Sani Usman ne ya bayyana hakan acikin wata takarda a garin Maiduguri, wani birnin jihar Borno.

KU KARANTA: LABARI MAI DADI: Rundunar sojin kasa ta kwace makamai daban-daban a yankin kudancin Kaduna (HOTUNA)

Manjo Muhammad Alkali, wani babban kwadinata na shalkwatar hukumar sojin Najeriya da kuma mukaddashin Janara Ofisha Kwamanda na hukumar sojin kasa ta dibishan 7 mai suna Victor Ezugwu ne janaral sojin kasa biyu da yan Boko Haram suka so kashe.

Su biyu sun fuskanta hare-haren bayan sun koma daga ziyarci dakarun sojin a wurin.

ALBISHIRINKU: Janaral sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram

Rundunar sojin kasa acikin dajin

“Sun fuskanta bama-bamai wadanda an binne a jamsin Banki da titin Pulka, tsawon kilomitar 6 zuwa garin Firgi a jihar Borno.

“Manyan ofishoshi biyu sun kai ziyara ga dakarun 26 Task Force Brigade da suka yi aikin Operation Lafiya Dole da kuma yakin Operation Deep Punch.” Inji Birigadiya janar Usman

Ku karanta ra'ayoyin yan Najeriya 3 akan abunda ya faru da janaral biyu.

Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Da anan https://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon yadda za'a murkushe yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel