Babachir: Buhari ya ba Osinbajo umarni cewa ya kori duk wanda aka samu da laifi

Babachir: Buhari ya ba Osinbajo umarni cewa ya kori duk wanda aka samu da laifi

– Kuna da labari cewa kwamitin da shugaban kasa ya nada ta binciki Babachir ta fara soma aiki

– Shugaba Buhari ya fadawa Farfesa Osinbajo cewa ka da ya daga kafa

– Shugaban kasa ya bada umarni cewa a hukunta duk wanda aka samu da laifi

Babachir: Buhari ya ba Osinbajo umarni cewa ya kori duk wanda aka samu da laifi

Farfesa Osinbajo zai binciki Babachir David Lawal

NAIJ.com na cigaba da kawo maku rahoto tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Babachir David Lawal tare bisa wasu zargi na saba doka wajen bada kwangila.

Kwamitin da aka nada tayi binciken ta cikin makonni biyu da shi mataimakin shugaban kasa zai jagoranta ta soma aiki. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa Osinbajo cewa ya hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa Osinbajo cewa ko na gida ne a daure

Babachir: Buhari ya ba Osinbajo umarni cewa ya kori duk wanda aka samu da laifi

Ba sani; ba sabo: Yadda za a binciki Babachir-Shugaban kasa

Yanzu haka dai Kwamitin ta tattara sunayen wadanda ake bukatar a gurfanar domin samun karin bayani. Shi kuwa shugaban kasar yace duk wanda aka samu da laifi a dakatar da shi ba tare da wata-wata tun kafin a kammala binciken.

Yanzu haka muna samun labari cewa an samu wasu karin manyan Jami’ai da rashin gaskiya da aka fara binciken. Tuni shugaba Buhari ya bada umarni a kora su daga matsayin su tun kafin a je ko ina.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa sun ce su na bayan Shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel