An tsoma fadar Kano cikin matsala

An tsoma fadar Kano cikin matsala

– Ana shirin fara binciken asusun Masarautar Jihar Kano

– Ana zargin fadar da kashe mahaukatan kudi wajen gudanar da sha’anin ta

– Sarki Muhammadu Sanusi II dai ya saba sukar shugabannin Yankin

An tsoma fadar Kano cikin matsala

Sarki Muhammadu Sanusi II da fadar Kano na cikin matsala

Dama tun kwanaki NAIJ.com ta kawo maku rahoto cewa Jama’a sun fara ganin cewa kalaman Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na nema yayi yawa ya wuce gona da iri. Har aka fara kishin-kishin din cewa ana kokarin sauke sa daga kujerar sa.

Wani Marubuci kuma Dan Jarida mai suna Ja’afar Ja’afar yayi wani rubutu inda ya bayyana irin kudin da fadar Kano ta rika batarwa wajen sayen manyan motoci da kuma hawa shafin yanar gizo.

KU KARANTA: Sojojin da su ka zama Sarakuna a Najeriya

An tsoma fadar Kano cikin matsala

Sarkin Kano Sanusi na II

Hukumar yaki da zamba da kuma karbar korafi ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bincikar Masarautar Jihar domin jin yadda aka kashe makudan biliyoyi cikin kankanin lokaci. Wani daga cikin manyan masarautar dai yace za su yi bayani ba da jimawa ba.

Kwamitin da aka nada tayi bincike game da su Babachir David Lawal ta soma aiki. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa Osinbajo cewa duk wanda aka samu da laifi a dakatar da shi ba tare da wata-wata tun kafin a kammala binciken.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarki Muhammadu Sanusi a wani bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel