Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba…-Shugaban APC Oyegun

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba…-Shugaban APC Oyegun

– Jam’iyyar APC ta ce shekaru 8 ba su isa a gyara Najeriya ba

– Shugaban Jam’iyyar yace ya zama dole shugaba Buhari yayi tazarce

– Oyegun ya bayyana irin abin da ke faruwa a APC

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa gaskiya fa shekaru 8 ba za su isa a gyara Najeriya.

Oyegun yace ya zama dole shugaba Muhammadu Buhari yayi tazarce.

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba…-Shugaban APC Oyegun

Shugaban APC Oyegun tare da Buhari

A wata hira da Cif Oyegun yayi kamar yadda NAIJ.com ta samu tattaunawar ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP tayi barnar gaske a kasar inda yace ko a cikin shekaru 8 shugaban kasa Buhari ba zai iya gama gyara Najeriya ba.

KU KARANTA: Buhari zai lashe zabe mai zuwa Inji APC

Buhari ba zai iya gyara Najeriya ba…-Shugaban APC Oyegun

Shekaru 8 sun yi kadan Buhari ya gyara Najeriya

Bayan cewa ya kamata shugaba Buhari yayi tazarce ya kuma bayyana irin matsalolin da Jam’iyyar ta ke samu na rashin kudi. Oyegun ya bayyana irin matakan da su ka dauka har da korar duk Dan Jam’iyyar da bai biyan kudin da aka kayyade na wata-wata.

A makon jiya ne Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta APC baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Muna bayan Buhari Inji 'Yan kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel