Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

– Farashin Naira na nan daram-dam-dam a kasuwa

– Dalar Amurka ta gagara wani yunkuri sama a kasuwar canji

– CBN na cigaba da taimakawa wajen tsagaita tashin dala

Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

Gwamnan babban bankin CBN

NAIJ.com ta dauko maku labari cewa darajar Dalar Amurka na dan yi kasa a karshen wancan makon. A da can Dalar Amurkar ta kara komawa kimanin N400 wanda yanzu ta sauko har zuwa N385 a kan kowace Dala guda.

To a haka dai aka rufe kasuwa karshen wannan makon inda Naira ta hana Dalar Amurka sakat. Yanzu dai haka farashin EURO ya koma N410 yayin da Pound Sterling na kasar Ingila ya koma N495.

KU KARANTA: Naira na cigaba da kara daraja

Tattalin arziki: Naira na cigaba da rike wuta

Naira ta hana Dala motsi

A kasuwar kasar waje dai an saida Dala ne a kan N315 zuwa N316. Kamar dai yadda muka ce a hannun ‘yan kasuwar Dalar tana kan N385. An dai samu sababbin tsare-tsare daga babban bankin kasar watau CBN bayan an kara sakin wasu makudan daloli a kasuwa.

‘Yan canji sun yi kira a rika sakin kudin kasar waje da Hukumar EFCC ta bankado zuwa cikin kasuwar domin abubuwa su kara rangwame.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya na cikin matsin tattalin arziki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel