Madalla: Shinkafa tayi mugun sauki

Madalla: Shinkafa tayi mugun sauki

– Farashin shinkafa yayi sauki a Jihar Kaduna

– Ana saida buhun shinkafa a kan N11000

– Wata kungiya ce dai da wannan kokari

Madalla: Shinkafa tayi mugun sauki

Buhun Shinkafa yayi mugun sauki

NAIJ.com na samun labari cewa yanzu haka an fara saida buhun shinkafa a kan kudi N11, 000 a Garin Kaduna. Farashin buhun shinkafa dai ya fi haka tsada tun bayan da aka shigowa da ita cikin kasar.

Wata kungiya mai zaman kan ta ce dai ta ke saida wannan shinkafa araha banza kan N11, 000 yayin da ake saida na kasuwa kan kusan N17, 000. Wasu ‘yan kasuwar dai sun kai kara wajen ‘yan sanda inda su kace ana saida buhu kasa da ainihin farashin sa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe wani Dattijo a Sokoto

Madalla: Shinkafa tayi mugun sauki

Kwastam sun datse buhunan Shinkafa

Tun ranar Litinin dai aka fara saida wannan shinkafa a daidai layin nan na Gamagira a Kasuwar barci da ke cikin Garin Kaduna. Mutane da dama dai sun taru domin samun na su buhun da wani dan kasuwa mai suna Sudais yake saidawa.

Kwanaki wani Darekta a Ma’aikatar yada labarai na Najeriya ya rubuta wasika ga Hukumar kwastam ta kasa inda yake bayyana mata cewa wasu na cigaba da shigo da shinkafa makare a boye cikin kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana shirin rusa gidajen wasu talaka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel