Kwamacala: Yadda wanda shugaba Buhari ya sallama ta ki barin ofis

Kwamacala: Yadda wanda shugaba Buhari ya sallama ta ki barin ofis

– Kwanaki Gwamnatin tarayya tayi wata zazzaga

– Shugaba Buhari ya sallami shugabannin Hukumomi da dama

– Haka kuma dai an nada sababbi nan-take

Kwamacala: Yadda wanda shugaba Buhari ya sallama ta ki barin ofis

Shugaban PENCOM ta ki barin Ofis bayan Buhari ya tsige ta

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku labari cewa shugaba Buhari ya sallami shugabannin Hukumomi da cibiyoyin Gwamnatin tarayya sama da 20 inda har ta kai Jama’ar Yankin Basawa da Samaru suka ce ba su yarda da sabon shugaban cibiyar bincike da nazari na NARICT.

Yanzu haka dai an yi ba girma-ba arziki tsakanin tsohuwar shugabanr Hukumar fansho ta kasa Anohu-Amazu inda ta ki barin Ofis har Ranar Juma’a. Har dai ta kai Hukumar DSS sun zo domin su cincibe ta daga Hukumar.

KU KARANTA: Magu ya bayyana gaban Osinbajo

Kwamacala: Yadda wanda shugaba Buhari ya sallama ta ki barin ofis

Ana nema a kora shugabar Hukumar fansho da karfin tsiya

Wata majiya dai na cewa Mrs. Anohu-Amazu tace babu wanda ya sanar da ita cewa an tsige ta. Akwai wanda ya bayyana cewa dama ta tafka badakala lokacin da aka nada ta a mulkin Goodluck Jonathan.

Har wa yau Farfesa Idris Muhammad Bugaje wanda tuni dai wa’adin sa ya kare a matsayin shugaban cibiyar nazari na NARICT ya rasa Mahaifiyar sa kwanan nan. An nada Farfesa Jef. T Barminas sai dai Jama’a sun ce ba su so.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tattalin arziki: Shin Buhari ya fitar da Najeriya daga matsi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel