An soma binciken Babachir David Lawal

An soma binciken Babachir David Lawal

– Kwamitin da shugaban kasa ya nada ta binciki Babachir ta fara shirin aiki

– Farfesa Osinbajo ya fara tattara wadanda ake bukatar a gayyata

– Tuni dai har an zauna da Magu na EFCC

An soma binciken Babachir David Lawal

Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa makon jiya

Kwanaki NAIJ.com ta kawo maku rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal tare da shugaban Hukumar NIA mai leken asiri bisa wasu zargi dabam-dabam.

Tuni aka nada kwamiti domin binciken su Mr. Babachir David Lawal inda mataimakin shugaban kasa zai jagoranta kuma har an soma aiki. Yanzu haka dai Kwamitin ta tattara sunayen wadanda ake bukatar a gurfanar domin samun karin bayani.

KU KARANTA: Babachir: Babu daga kafa Inji Garba Shehu

An soma binciken Babachir David Lawal

Osinbajo na binciken Babachir

Har dai Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu tun kwanaki inda aka dauki lokaci ana masa tambayoyi. An dai bayyana cewa a boye za a yi binciken ba tare da kowa ya ji ba.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa dai za ayi adalci wajen binciken kuma babu daga kafa ko kadan. A baya dai Hukumar NLC ta bayyana cewa bai dace ace mataimakin shugaban kasa bane zai binciki sakataren Gwamnatin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Muna bayan Buhari Inji 'Yan Kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel