Muna bukatan wani shugaban kasa, miyagu sun kwace gwamnatin Buhari - Junaid Mohammed

Muna bukatan wani shugaban kasa, miyagu sun kwace gwamnatin Buhari - Junaid Mohammed

-Wani dan arewa mai adawan Buhari ya sake Magana akan shugaban

-Yace yan Najeriya sun gaji da mulkin Buhari kuma ba zasu sake zabanshi ba

Wani tsohon dan majalisa, Junaid Mohammed, yayi ikirarin cewa wasu miyagu a Aso Rock sun kwace mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari.

Junaid ya baiwa Buhari shawaran cewa ya manta da zancen cewa zai yi tazarce saboda yan Najeriya sun gaji da salon mulkinsa kuma ba zasu sake zabensa ba.

Ya bayyanawa manema labarai a ranan Juma’a a Abuja cewa abin kunya ne Buhari ya bari wasu yan tsiraru su kwace masa gwamnati ta hanyar yin abinda ke sabanin bukatun mutane.

Muna bukatan wani shugaban kasa, miyagu sun kwace gwamnatin Buhari - Junaid Mohammed

Muna bukatan wani shugaban kasa, miyagu sun kwace gwamnatin Buhari - Junaid Mohammed

Yace : “Miyagun da e karkashin shugaba Buhari sun kwace dukkan al’amuran kasan nan daga hannunsa kuma sun gagareshi, kuma wannan abu ne mai hadari ga Najeriya.

“Kamar yadda ya bayyana, Buhari bay a iya yanke shawara akan wadannan miyagu masu gudanar da gwamnatinsa wadanda ke bin son ransu. A karshe, shugaba Buhari na kokain lallashin miyagun ne maimakon yan Najeriya.

KU KARANTA: An gano makudan kudi a gidan Danjuma Goje

“Saboda haka , wanna kasa na bukatan shugaban wanda baida kalubalen addini, kabila, da lafiyar jiki ta shugabanceta.”

Zaku tuna cewa mataiakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa shi bai san wasu miyagu a gwamnatin Buhari ba, bal shi ma nemansu yakeyi.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel