Babu wanda Buhari zai dagama kafa – Garba Shehu

Babu wanda Buhari zai dagama kafa – Garba Shehu

-Malam Garba Shehu yayi magana zancen dakatad da SGF

Mai Magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu yayi hira da jaridar Daily Trust akan abubuwan da suka faru aka dakatad da sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal da diraktan hukumar NIA, Ambasada Ayo Oke.

Zaka iya mana fashin baki akan abubuwan da ke tattare dakatad da SGF da shugaban NIA?

“ Jawabin da aka saki ranan Laraba, yayi bayani filla-filla akan cewa shugaban kasa ya yanke shawaran gudanar da bincike da kansa bayan majalisan dokokin tarayya tayi bincike kuma bayar da sakamakon bincikenta. Shugaban kasan ya aika wasika ga majalisar datawa akan cewa sakataren yace ba’a bash daman fadin albarkacin bakinsa kafin aka yada shi ba. Anan ne aka samu matsala, shi sakataren yace zai je kotu amma daga baya kuma ya bayyana gaban majalisan. Majalisan ta sanya ranan da zai zo amma kuma ta sake dagawa.

Babu wanda Buhari zai dagama kafa – Garba Shehu

Babu wanda Buhari zai dagama kafa – Garba Shehu

Kila shugaban kasan yayi niyyan gudanar da bincike da kansa; har yanzu majalisar dattawa bata bada rahoton ta na karshe na. amma la’alla cikin makonni biyu na kwamitin mataimakin shugaban kasa, ajalisar dattawa ta shirya nata rahoton.

KU KARANTA: DSS ta kai simame ofishin Pencom

Game da zancen NIA, kun san anyi bayanai a cikin jawabin. Shugaban kasa na bukatan sanin wanda ya bada wannan makudan kudin- yadda tazo da kuma yadda aka samo ta? An boye a wata gida- na waye? Me zasuyi da shi?”.

“Yayinda ake gudanar da bincike, ya bukaci kowa ya kebe gefe. Komai na cikin jawabin.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel