Shugaban kasa ya maidawa Babachir martani

Shugaban kasa ya maidawa Babachir martani

– Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa makon jiya

– Babachir din bai yarda da cewa an tsige sa ba da farko

– Sai dai fadar shugaban kasa tace gatse ne kurum yake yi

Shugaban kasa ya maidawa Babachir martani

Shugaban kasa ya dakatar da Babachir

NAIJ.com ta kawo maku rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal bisa wasu zargi na bada kwangiloli ba tare da ka’ida ba.

Sai dai Mr. Babachir David Lawal din ya nuna cewa bai ma san an dakatar da shi da farko ba. Babachir Lawal ya maidawa ‘Yan jarida tambaya inda yake cewa wane shugaban kasar ne ya dakatar da shi lokacin da aka yi masa tambaya.

KU KARANTA: Dr. Lawal ta maye gurbin Babachir Lawal

Shugaban kasa ya maidawa Babachir martani

Shugaban kasa tare da Mr. Babachir a da

Fadar shugaban kasa ta bakin Malam Garba Shehu na cewa ba burin shugaba Muhammadu Buhari ba ne ce-in-ce da Sakataren da aka dakatar daga aiki. Shi kuwa Femi Adesina ya bayyana cewa gatse ne kurum na Mr. Babachir.

Shugaba Buhari ya nada kwamiti domin tuhumar Sakataren Gwamnatin kasar kana Dr. Habiba Lawal za ta maye gurbin na sa zuwa wani lokaci. An dai ga Babachir yana gwalo lokacin da zai bar fadar shugaban kasa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan kasuwa na bayan Shugaba Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel