Ibrahim Magu ya gabatar da hujja gaban kwamitin bincike akan kudin da aka gano

Ibrahim Magu ya gabatar da hujja gaban kwamitin bincike akan kudin da aka gano

- Shugaban hukuar EFCC, Ibrahim Magu, ya gabatar da hujja akan harin da suka kai daki mai lamba 7b Osbourne Towers. Ikoyi Legas

- Magu, Monguno da Malami sun gana bayan bayyana da Magu yayi gaban shugaban kasa a masallacin Juma’a

- Anyiwa Magu tambayoyi da dama inda ya kwashe awowi har mislain karfe 4 na rana a jiya Juma’a

Kwamitin da shugaba Buhari ya nada akan bincike bayan dakatad da sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, da shugaban hukumar NIA, Ayodele Oke, ta fara aikinta da gayyatar shugaban hukumar hana alundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC Ibrahim Magu.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Magu ya bayyana gaban kwamitin ne ranan Juma’a, 21 ga watam Afriu karkashin jagorancin mataimakin shuagban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami da kuma NSA, Babagana Munguno.

Ibrahim Magu ya gabatar da hujja gaban kwamitin bincike akan kudin da aka gano

Ibrahim Magu ya gabatar da hujja gaban kwamitin bincike akan kudin da aka gano

An samun rahoton cewa anyiwa Magu tambayoyi game da kudi N13bn da aka gano a Legas wanda tsohon shugaban NIA, Ayo Oke yace na hukumar NIA ne.

KU KARANTA: Kamfanin sadarwan MTN tayi kashaidi ga masu sayarda katin waya

Wani babban jami’in gwamnati wanda aka sakate sunansa yace a tambayi shugaban hukumar akan harin binciken kuma ya gabatar da hujjansa akan hakan.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel