Kungiyar Amnesty Watch tace akalla mutane 55 sun hallaka a kurkukun soji

Kungiyar Amnesty Watch tace akalla mutane 55 sun hallaka a kurkukun soji

Wata kungiyar yakin kwato hakkin dan adam, Global Amnesty Watch Foundation, ta bayyana cewa akalla mutane 55 ne suka ras rayukansu a firsinan soji da ke Barikin Giwa a Maiduguri hgarin gudanar da bincike akansu.

Kana kungiya Amnesty International ta siffanta barikin Giwa a matsayin wajen mutuwa yayinda suka tuhumci rundunar sojin Najeriya da tsare wadanda ake zargi da Boko Haram inda aka mutane 240 sun hallaka hadi da yara 29.

Amma, hukumar soji ta karyata wannan rahoton.

Mutane 55 sun hallaka a kurkukun soji a Maiduguri – Amnesty Watch

Mutane 55

A wata binciken da jakadiyar kungiyar Global Amnesty Watch Foundation, Helen Adesola tayi inda tayi bayani a wata hira da yan jarida cewa mutane 55 ne suka hallaka a firsinan soji a Maiduguri.

KU KARANTA: Za'a sake daukan sabbin jami'an yan sanda 155,000

Game da cewarta, wadannan mutane sun hallaka ne kafin mika wasu da ake zargi da Boko Haram 593 da hukumar soji ta mikawa gwamnatin jihar Borno.

Mrs Adesola ta kara da cewa a binciken da suka gudanar na sanin sanadiyar mutuwansu, an samu samu sun hallaka bisa azaban zafi sabanin ciwon sankarau da akace.

“A likitance, maganin azabar zafi shine samarwa firsinonin isak isasshe da ruwa.

“Irin wannan kurkukun kamar sauran da ke irin wannan abu suna bukatan Karin kayayyakin aiki wajen tabbatar da koshin lafiyan fursinoni maras lafiya,”

Tayi kira ga gwamnatin jihar Borno da su kasance kan gaba wajen gyara rayuwan kutane 593 da aka mika musu wadanda yan asalin jihar Borno ne yawancinsu.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel