Lawal Daura da Ibrahim Magu sun kebe a fadar shugaban kasa ta Aso Rock

Lawal Daura da Ibrahim Magu sun kebe a fadar shugaban kasa ta Aso Rock

- Shugaban hukumar DSS ta kasa Lawal Daura, da Shugaban riko na hukumar EFCC Ibrahim Magu, sun kebe gaba da gaba inda suka yi ganawar sirri a fadar Shugaban kasa dake Aso Rock Abuja

- An samo daga Majiyar mu da ta rawaito mana cewa bayan ganawar tasu kuma tare suka yi sallar Jumu'a da Shugaban kasa a masallacin dake cikin gidan gwamnatin

In mai sauraro zai iya tunawa hukumar DSS ce ta turawa majalissar tarayya, rashin gamsuwarta a kan Magu wajen tantance ce a zama Shugaban hukumar EFCC mai cikakken iko.

Wanda ita kuma majalissar ta kafa hujjar kin tantance shi bisa ruhoton DSS din da suka aiko masu, cewar NAIJ.com.

Mi kuke tunanin suka tattauna a kebewar tasu?

Lawal Daura da Ibrahim Magu sun kebe a fadar shugaban kasa ta Aso Rock

Lawal Daura da Ibrahim Magu sun kebe a fadar shugaban kasa ta Aso Rock

KU KARANTA: Wani matashi dan shekara 23 ya kashe kansa a Sokoto

A wani labarin kuma, Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi Kira ga gwamnatin Tarayya da ta dai na fakewa da wadansu abubuwa domin boye gazawarsu kan kawo karshen rikicin Fulani Makiyaya da mazauna wasu garuruwa a fadin Kasa Najeriya.

Dayake hira da manema labarai a shirin da kungiyar ta keyi na fara yin wata taron gangami na kwana biyar a Abuja shugaban shirya taron kuma Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle yace ayyukan Fulani a wasu sassan kasa Najeriya ya nuna cewa matsalar ya fi karfin gwamnati.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu yan Najeriya ne ke tsokaci game da tattalin arzikin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel