Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade a kwalejojin kimiya da fasaha na tarayya

Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade a kwalejojin kimiya da fasaha na tarayya

- Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanya hannu a kan sunayen sabbin mukaman da ya nada wadanda za su ja ragamar manyan kwalejojin kimiya da fasaha na tarayya, (Federal Polytechnic) guda 21 dake fadin kasar nan

- Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai yau a birnin tarayya Abuja

Ya ce sabbin shuwagabannin za su taimaka wajen aiyukan gudanarwa na kwalejojin wajen tabbatar da bin doka da oda da aka gina makarantun a kansu.

Wadanda aka nada din kuwa akwai:

JT Orkar, Akanu Ibiam Federal Polytechnic Unwana, da Afikpo Michael Oloko, Auchi Polytechnic, Auchi da Austin Adeze, Federal Polytechnic, Ado Ekiti sannan kuma Yalwa Tahir, Federal Polytechnic, Bali.

NAIJ.com sun samu labarin sauran sun hada da Abubakar Dantata, Federal Polytechnic, Bauchi; da Muhammad Yakya, Federal Polytechnic, Bida; da Mohammed Abubakar, Federal Polytechnic, Damaturu; da kuma Nasir Yauri, Federal Polytechnic, Ede.

Haka kuma akwai Olanipekun, Federal Polytechnic da Ekowe; Ibrahim Liman Sifawa, Federal Polytechnic, Idah; da Abubakar Sadauki, Federal Polytechnic, Ilaro ;da Odey Ochicha, Federal Polytechnic, Ile-Oluji da kuma Kingsley Alagoa, Federal Polytechnic, Kaura Namoda.

Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade a kwalejojin kimiya da fasaha na tarayya

Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade a kwalejojin kimiya da fasaha na tarayya

Ya kuma kara bayyana Bassey Usang Bassey a matsayin wanda zai jagoranci shugabancin Federal Polytechnic, Mubi; da Godwin Sogolo, Federal Polytechnic, Nasarawa; da Edwin Ogunbor, Federal Polytechnic, Nekede, Owerri; da Osekula Zikora, Federal Polytechnic, Offa sai kuma Lasbury Amadi, Federal Polytechnic, Oko.

KU KARANTA: Naira na ci gabada kara daraja

Samu labarin sauran kuwa sun hada da Ucha Julius, Federal Polytechnic of Oil da Gas, Bonny; da Ike Udabah, Federal Polytechnic, Ukana; da Abayomi Daramola, Hussaini Adamu Federal Polytechnic, Kazaure; da kuma Yusuf Hassan, Kaduna Polytechnic, Kaduna.

Akwai David Adewunmi, National Institute of Construction Technology, Uromi; da Ismail Biodun Layi Oni, Waziri Umaru Federal Polytechnic, Birnin-Kebbi; da Lateef Fagbemi, Yaba College of Technology, Yaba.

Ya bayyana cewa za a rantsar da su su kama aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu yan Najeriya ne ke shan alwashin zabar Buhari a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel