Rikicin Fulani da Manoma: An kai mu makura inji kungiyar Kiristoci

Rikicin Fulani da Manoma: An kai mu makura inji kungiyar Kiristoci

- Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi Kira ga gwamnatin tarayya da ta dai na fakewa da wadansu abubuwa domin boye gazawarsu kan kawo karshen rikicin Fulani makiyaya da mazauna wasu garuruwa a fadin Kasa Najeriya

- Dayake hira da manema labarai a shirin da kungiyar ta keyi na fara yin wata taron gangami na kwana biyar a Abuja shugaban shirya taron kuma shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle yace ayyukan Fulani a wasu sassan kasa Najeriya ya nuna cewa matsalar ya fi karfin gwamnati

Jaridar NAIJ.com ta tsinkaye su suna cewa: “A makon nan kawai Fulani sun kashe mutane 30 a kauyukan kudancin Kaduna.

“A shekarar da ta gabata gwamnati ta sanar da kafa wata rundunar soji ta musamman domin yaki da masu tada zaune tsaye a yankunan amma duk da wannan shiri na gwamnati an ci gaba da samun kashe-kashen mutane a yankunan.

“Irin yadda jami’an tsaro suka yi maza-maza wajen kamo wadanda ke da hannu a rikicin Ile-Ife bamu ga haka ba a na Fulani makiyaya da suka addabi mazauna garuruwa da dama a kasar nan.

Rikicin Fulani da Manoma: An kai mu makura inji kungiyar Kiristoci

Rikicin Fulani da Manoma: An kai mu makura inji kungiyar Kiristoci

“Muna kira ga gwamnati da su kara kaimi wajen ganin an kawo karshen wannan kashe kashe da Fulani makiyaya sukeyi domin a gaskiya an kaimu makura yanzu.

KU KARANTA: Jigo a jam'iyyar APC yayi fito na fito da Cif Oyegun

“Muna jinjina wa gwamnati da sojojin Najeriya kan kokarin da ta keyi wajen ganin an kawo karshe ayyukan Boko Haram a Kasa Najeriya.''

Ya kuma ce gwamnati ta duba yadda take raba mukamen gwamnati da lura da daidaita rabon ga addinan kasarnan yadda ya kamata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli wasu yan Najeriya na cewa zasu zabi Buhari a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel