Kuzo ku ceci APC yanzu, Frank ya roki Buhari, Osinbajo, da sauran jigogi

Kuzo ku ceci APC yanzu, Frank ya roki Buhari, Osinbajo, da sauran jigogi

-Wato sabuwar rikici ta kunno kai a cikin jam’iyyar APC

-Mataimakin kakakin jam’ iyyar yana cigaba da adawa da shugaban jam’iyyar John Odigie-Oyegun

Wani mamban jami'yyar All Progressives Congress (APC), Mr Timi Frank, yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari , mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugabancin majalisan dokoki su ceci jam’iyyar daga kifewa.

Wasu jigogin jam’iyyar da ya ambata a jawabin da ya saki ranan Juma’a a Abuja ta kunshi Asiwaju Bola Tinubu da Alh. Atiku Abubakar.

Kana kuma da sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar domin su ceci rayuwar jam’iyyar.

Kuzo ku ceci APC yanzu, Frank ya roki Buhari, Osinbajo, da sauran jigogi

Kuzo ku ceci APC yanzu, Frank ya roki Buhari, Osinbajo, da sauran jigogi

Frank ya saki wannan jawabi ne bisa ga daga taron ganawar shugabannin jam’iyyar da kwamitin aikin jam’iyyar NWC tayi.

Kwamitin aikin jam’iyyar a wata jawabin da kakakin jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya saki ranan Alhamis ta alanta daga taron ganawar bisa ga wasu dalilai.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci sallar Juma'a yau

Tace za’a sanar da jama’a akan sabon ranan da za’a zaba domin ganawar.

Amma Frank, ya ga laifi cikin daga taron kuma yace wannan dalilan rashin amincewarsa shugaban jam’iyyar John Odigie-Oyegun, da kuma salon shugabancinsa.

Yace shugabannin jam’iyyar basu komai domin neman cigaban gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel