Buhari ya naɗa shuwagabannin hukumar cigaban arzikin ma’adanan ƙasa

Buhari ya naɗa shuwagabannin hukumar cigaban arzikin ma’adanan ƙasa

- Shugaba Buhari ya nada sabbin shuwagabannin hukumar kula da ma'adanan kasa

- Hukumar zata amfana daga bashin dala miliyan 150 da bankin duniya ta baiwa Najeriya

A cikin sharuddan bankin duniya na baiwa Najeriya rancen dala miliyan 150 don inganta harkar hakan ma’adanan kasa, gwamnatin Najeriya tayi garanbawul ga shugabancin hukumar cigaban arzikin ma’adanan kasa.

Ministan ma’adanan kasa Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA:Koriya ta Arewa tayi atisayen nuna ƙwanji don shirin yaƙi da Amurka (Hotuna/bidiyo)

Sanarwar data samu sa hanun babban sakataren ma’aikatan kula da ma’adanai, Mohammed Abbas tace shugaba Buhari ya amince da nada Uba Saidu Malami kwararre a harkar sanin ma’adanai a matsayin shugaban hukumar.

Buhari ya naɗa shuwagabannin hukumar cigaban arzikin ma’adanan ƙasa

Uba Saidu Malami

Yayin aka sanar da sunan kwamishiniyar kasuwanci da cinikayya ta jihar Zamfara Hajiya Ftaima Shinkafi Ibrahim a matsayin sakatariyar hukumar.

Buhari ya naɗa shuwagabannin hukumar cigaban arzikin ma’adanan ƙasa

Haj Fatima

Minista Fayemi yace za’a yi amfani da kudin da aka ciyo bashin ne wajen horar da masu sana’ar hake haken ma’adanai, musamman kananan masu hako ma’adanan kasa. Ministan ya kara da fadin, hakan zai magance hake hake ba bisa bin doka ba, zai habbaka zuba jari a fannin tare da samar da daman karkatar da tattalin arzikin kasa.

Buhari ya naɗa shuwagabannin hukumar cigaban arzikin ma’adanan ƙasa

Minista Fayemi tare da Buhari

NAIJ.com ta tattaro sunayen sauran shuwagabannin da aka nada a hukumar kamar haka: Demola Gbadegesin daga jihat Oyo, Theo Iseghohi daga jihar Edo, Samuel Eze daga jihar Ebonyi, Uwatt Bassey Uwatt daga jihar Akwa Ibom sai Yinka Mubarak.

Sanarwar ta kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli abinda yan kasuwa ke fadi akan Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel