Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

- Yan Boko Haram sun hallaka wani soja watanni kadan da yin bikinsa

- Kimanin watanni biyu da suka gabata ne aka daura auren wannan marigayin soja

Mayakan Boko Haram sun hallaka wani matashin soja kuma sabon ango, Muhammad Abdullahi da aka fi sani da suna Kamal a wani mummunan hari da suka kai garin Damboa na jihar Borno.

Abokin Kamal mai suna Musa Sa'idu Adam ne ya sanar da mutuwar abokin nasa a shafin sadarwar zamani na Facebook.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

Shi dai wannan soja ya gamu da mutuwarsa ne kimanin watanni biyu bayan an daura masa aure da masoyiyarsa yar garin Damboa, inda a garin na Damboa ne aka sha bikin auren nasu tare da abokan aikinsa sojoji.

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Marigayin

A wani labarin kuma anyi wata kazamar artabu tsakanin mayakan rundunar Boko Haram dana dakarun sojojin Najeriya inda aka kwashe sama da awanni 2 ana musayar wuta.

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Sojan a ranar bikinsa

Wannan karan battana ta faru ne yayin da sama da ‘yan Boko Haram 200 suka far ma wata bataliyan sojojin Najeriya a bazata in da suka kashe sojoji 8 sannan suka raunata wadansu 11.

Sai dai kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito, mayakan Boko Haram din sun yi wa bataliyan sojin shigar ba za ta ne.

Ga sauran hotunan:

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Marigayi

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Katin aurensa

Boko Haram sun kashe wani jarumin soja watanni 2 bayan aurensa (Hotuna)

Kamal tare da abokinsa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa suna goyon bayan Buhari, kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel