Akalla yan kallon kwallo 30 ne suka hallaka a gidan kallo

Akalla yan kallon kwallo 30 ne suka hallaka a gidan kallo

- Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayinda wayan wuta ya rikito kan kwanon gidan kallon kwallo

- Wata majiya tace mutane 80 ne ke cikin gidan kallon kwallon yayinda abin ya faru

Sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayinda wayan wuta ya rikito kan kwanon gidan kallon kwallo a garin Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Game da cewar talabijin Channels, yan kallon kwallo sun taru a gidan kallon kwallon domin kallon wasan Manchester United da Anderlecht a daren Alhamis.

Akalla yan kallon kwallo 30 ne suka hallaka yayinda suke kallon wasan Manchester United da Anderlecht a jihar Cross River

Akalla yan kallon kwallo 30 ne suka hallaka yayinda suke kallon wasan Manchester United da Anderlecht a jihar Cross River

Wanni wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyanawa jaridar Punch cewa wata transfoma da ke kusa da Iyang-Esu a karamar hukumar Calabar tayi bindiga lokacin da ake wasan wanda ya sabbaba faduwar wayan wuta kan kwanon gidan kallon kwallon.

KU KARANTA: Abinda da Jonathan yayi niyyan yi da kudin Ikoyi

Yace: “ Ya faru ne yayinda ake wasan Manchester United da Anderlecht. Naji karan wata bugawa. Kawai sai na fita duba abinda ya buga. Dawowa na ke da wuya, sai naga wayan na fadowa kan kwanon gidan kallon wanda ya hallaka mutanen da ke ciki."

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel