Gwamnonin jihohi 6 cikin 36 ne kawai suka biya kudin fansho

Gwamnonin jihohi 6 cikin 36 ne kawai suka biya kudin fansho

-An yabawa gwamnan jihar Legas, Jigawa, Flato, Ogun, Yobe da Anambra

- Kungiyar yan fansho tace wadannan kadai ne suka cancanci lambar yabon kungiyar

Gamayyar yan fanshon Najeriya, NUP tace gwamnoni 6 cikin 36 kacal ne ba’a bin bashin kudin fansho.

Wannan na kunshe cikin jawabin da kakakin kungiyar ya rattaba hannun, Kwmred Bunmi Ogunkolade.

Gamayyar wacce wata reshen kungiyar kwadagon Najeriya ne NLC, kuma mai kwato hakkin yan fansho gajiyayyyu sun bayyana cewa gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ; gwamnan jihar Osun, Ibikunle Amosun; da gwamnan jihar Jigawa, Abdullahi Badaru ne suka biya kudin fansho cikakke.

KU KARANTA: Amfanin Zogale da lafiyar dan Adam

Sauran kuma sune gwamnan jihar Flato, Simon Lalong; gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam.

Gwamnonin jihohi 6 cikin 36 ne kawai suka biya kudin fansho

Gwamnonin jihohi 6 cikin 36 ne kawai suka biya kudin fansho

NUP tace gwamnonin 6 zasu karba lambar yabo na kokari da kuma kula da yan fanshi a taron gangamin da za’ayi ranan Laraba mai zuwa inda zasuyi zaben sabbin shugabannin kungiyar.

Ogunkolade yace gwamnoni 6 sun fifita yan fanshi sosai kuma sun cancanci lambar yabo.

Kana kuma zasu tattauna yadda zasu yi da gwamnonin da suke kin biyan kudin fansho da gayya a taron.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel