Gasar zakarun nahiyar turai: Real Madrid zata gwabza da kishiyarta, Athletico Madrid

Gasar zakarun nahiyar turai: Real Madrid zata gwabza da kishiyarta, Athletico Madrid

- Real Madrid zata sake fuskantar Athletico Madrid a wasa na biyu dana karshe na gasar zakarun nahiyar turai

- Yayinda Juventus aka hada ta da kungiyar AS Monaco

A ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu ne aka yi hade haden wasa na biyu da karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a birnin Swiss.

A wannan karon ma an sake hada kungiyar Real Madrid da kishiyarta da Athletico Madrid, don fafatawa a neman gurbin shiga wasan karshe, yayin da kungiyar kwallon kafa ta Juventus zata gwada kwanji da Monaco ta kasar Faransa.

KU KARANTA: Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam

Dukkanin wasannanin guda 2 za’a buga su ne a watan gobe. Wannan haduwar na Real Madrid da Athletico Madris bay au farau ba, don ko kakar wasa data gabata sun hadu a wasan karshe, inda Real ta lashe gasar a bugun daga kai sai gola.

Gasar zakarun nahiyar turai: Real Madrid zata gwabza da kishiyarta, Athletico Madrid

Cristiano Ronaldo

Haka zalika kungiyoyin biyu sun hadu a wasan karshe na kakar wasa 3 da suka gabata, inda Real ta sake lashe gasar a mintunan kari.

Gasar zakarun nahiyar turai: Real Madrid zata gwabza da kishiyarta, Athletico Madrid

Griezmann

Idan ba’a manta ba dai Madrid ta lallasa Bayern Munich ci 6 da 4 a wasan zagaye na uku, amma dai a wannan kakar wasa, Madrid ce zata fara karbar bakuntar Athletico Madrid, daga bisani sai a rama biki a gidan Atheltico.

Gasar zakarun nahiyar turai: Real Madrid zata gwabza da kishiyarta, Athletico Madrid

Yan wasan Juventus

Itama kungiyar Juventus ta taba fafatawa da Monaco a wasan zagayen na uku a kakar wasa na shekarar 2014-2015, kamar yadda NAIJ.com ta samu bayanai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan matan Najeriya yan kwallo sun koka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel