Babachir: NLC ta hurowa Mataimakin shugaban kasa wuta

Babachir: NLC ta hurowa Mataimakin shugaban kasa wuta

– Kwanan nan Shugaba Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin sa

– Shugaba Buhari ya nada Osinbajo yayi bincike game da laifin da ke kan Babachir Lawal

– Sai dai Kungiyar kwadago tace bai dace Osinbajo ya binciki Babachir ba

Babachir: NLC ta hurowa Mataimakin shugaban kasa wuta

Kungiyar kwadago tace Osinbajo bai isa ya binciki Babachir ba

Dazu NAIJ.com ke kawo maku cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Dr. Habiba Lawal wanda za ta maye gurbin na Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal da aka dakatar.

Shekaran jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal bisa wasu zargi na bada kwangiloli ba tare da ka’ida ba. Shugaba Buhari ya nada kwamiti domin tuhumar Sakataren Gwamnatin kasar.

KU KARANTA: Ya zama dole a tarkata Babachir-Sagay

Babachir: NLC ta hurowa Mataimakin shugaban kasa wuta

An hurowa Mataimakin shugaban kasa wuta game da SGF

Sai dai Sakataren kungiyar kwadago na kasa Dr. Peter Ozo-Eson yace ba Mataimakin shugaban kasa ya kamata a sa ya binciki Babachir din ba. Dr. Ozo-Eson yace an yi daidai da aka dakatar da Babachir da shugaban Hukumar NIA sai dai ba Osinbajo ya kamata yayi binciken ba.

An dai dakatar da Mr. Babachir bisa zargin ba da kwangila ba tare da ka’ida ba sannan kuma an dakatar da shugaban Hukumar NIA Ambasada Ayodele Oke,

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnatin Buhari: Najeriya na fama da matsin tattali

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel