Koriya ta Arewa tayi atisayen nuna ƙwanji don shirin yaƙi da Amurka (Hotuna/bidiyo)

Koriya ta Arewa tayi atisayen nuna ƙwanji don shirin yaƙi da Amurka (Hotuna/bidiyo)

- Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya shirya tsaf don gamawa da kasar Amurka da makamin kare dangi

- Amurka ta nemi hadin gwiwar kasar Sin domin yakar kasar Koriya ta Arewa

Gwamnatin kasar Koriya ta kudu tace a shirye take ta aika da makami mai linzami kasar Amurka muddin Amurka tayi gangancin gangan wajen haye mata.

Kasar Koriyan ta bayyana haka ne a shafin jaridar gwamnati, inda tace ‘Harin gargadi kadai ya isa ya rugurguza kasar Amurka gaba daya’ kamar yadda majiyar NAIJ.com, Reauters ta ruwaito a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Kadan daga cikin gudummawar da Ahmadu Chanchangi ya bayar domin cigaban Musulunci da Al'umma

“Idan suka sake muka aika musu da makami mai linzami a harin gargadi kawai, toh ya isa ya lalata Amurka gaba daya da sojojin Amurka dake Koriya ta kudu” inji jaridar Rodong Sinmun.

Koriya ta Arewa tayi atisayen nuna ƙwanji don shirin yaƙi da Amurka (Hotuna/bidiyo)

Shugaban kasar Koriya ta Arewa

A cikin satin nan kasar Koriya ta kudu tayi gwajin kwanji tare da gwajin makamen kare dangi, tare da cigaba da cika baki da musayar yawu da kasar Amurka.

Wannan bugun kirji na kasar Koriya ta kudu yazo ne a daidai lokacin da marigayi mahaifin shugaban kasa mai ci wato Kim II Sung ke bikin murnan zagayowar ranar haihuwarsa ne.

Koriya ta Arewa tayi atisayen nuna ƙwanji don shirin yaƙi da Amurka (Hotuna/bidiyo)

Makamin kare dangi mallakin kasar Koriya ta Arewa

Sai dai a nata bangaren, kasar Amurka ta koma tana hada kai da kasar Sin don yakar kasar Koriya ta Arewa, musamman yadda yayi amfani da gabar dake tsakanin kasashen biyu, amma fa Trumo yayi gargadin idan har kasar Din ta gagara daukan mataki akan Koriya ta Arewa, to zai yi shirin yaki da Koriyan shi kadai.

Kalli bidiyon atisayen gwajin kwanji da kuma bajakolin makamai da Koriya tayi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon yakin basasan Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel