Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

- Matasan kabilar Igbo dana Hausawa sun kai ma shugaban EFCC, Magu ziyara

- Sun jaddada goyon bayansu ga yaki da almundahana da cin hanci da rashawa

Kungiyar matasan Inyamurai mai suna ‘Ohaneze Youth Parliament’ dana matasan Arewa sun bayyana gamsuwarsu da kamun ludayin shugaban hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne yayin wata ziyara da suka kai ma shugaban EFCC a babban ofishin hukumar dake Abuja a ranar ALhamis 19 ga watan Afrilu, inda suka bayyana Magu a matsayin mutumin daya farfado da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

KU KARANTA: EFCC: Jami'an mu basu kai wani samame ba a gidan Sanata Danjuma Goje

Dayake jawabi, shugaban tawagar matasan Inyamurai Okonkwo Patrick yace “EFCC a karkashin jagorancin Magu sun samu dimbin nasarori daban daban, don haka wannan yaki da ake yi da cin hanci da rashawa ban a Magu bane kadai, ya kamata kowannen mu ya bada tasa gudunmuwar.”

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

Shugaban matasan tare da Magu

Patrick ya cigaba da fadin “Magu ya kawo sauyi mai inganci a yanayin aikin hukumar EFCC, tare da tsanstane, gaskiya da rikon amana, mu matasan Najeriya, mune zamu amfana daga aikin da Magu yake yi na magance cin hanci da rashawa.”

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

Zaman Magu da matasan Hausawa da Inyamurai

Daga bisani NAIJ.com ta ruwaito Mista Patrick Okonkwo ya mika takardar shaidar jarumta ga shugaban EFCC, Ibrahim Magu

A nasa jawabin, Magu ya gode ma kungiyar matasan, musamman kan gamsuwa da yadda yake gudanar da aikinsa, sa’annan ya tabbatar musu cewar zai dage wajen cigaba da aikinsa ba tare da tsoro ba.

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

Patrick na mika ma Magu shaidar lambar yabo

“Na sha fada, ba mu muka fi kowa sanin yadda za’a magance cin hanci da rashawa ba, tunda matsalar nan ta addabi kowa da kowa, kamata yayi mu hada hannaye wajen yakarsa,” Inji Magu.

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa sun jaddada goyon bayansu ga Magu (Hotuna)

Kungiyoyin Inyamurai da Hausawa tare da Magu

Daga karshe Magu yayi kira ga yan Najeriya da a hada kai a yaki cin hanci da rashawa don samar ma yaranmu rayuwa mai kyau, sa’annan ya nanata cewa “Babu wanda ya isa ya dakatar damu daga yaki da cin hanci da rashawa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda EFCC ke yaki da cin hanci da rashawa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel