Kasurgumin dan Boko Haram daya hallaka mutane 150, ya miƙa kokon bara ga musulmai, karanta

Kasurgumin dan Boko Haram daya hallaka mutane 150, ya miƙa kokon bara ga musulmai, karanta

- Muhammad Nafiu kwamandan Boko Haram da aka kama a jihar Gombe ya nemi afuwa

- Nafiu ya amsa laifin hallaka sama da mutane 150 a garin Baga na jihar Borno

Jaridar Rariya ta dauko rahoton wani kasurgumin kwamandan Boko Haram da rundunar yansandan jihar Bauchi ta kama a ranar Laraba 19 ga watan Afrilu yace yayi nadamar aika aikan da yayi, don haka a yafe masa.

Shi dai wannan Kwamandan Boko Haram mai suna Muhammad Adamu Nafiu yana da shekaru 25, ya tsere ne daga dajin Sambisa bayan dakarub sojin kasa sun kwato dajin daga hannun Boko Haram tare da mamaye dajin.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

NAIJ.com ta ruwaito Nafiu dan asalin garin Balanga ne, na jihar Gombe, sa’annan bayan tserewarsa daga dajin Sambisa sai ya koma kauyen Tama, inda a nan ne dubun sa ta cika, bayan ya shiga hannun manyan jami’an tsaro.

Kasurgumin dan Boko Haram daya hallaka mutane 150, ya miƙa kokon bara ga musulmai, karanta

Nafiu yana nuna hotonsa

Bugu da kari Nafiu na cikin jerin yan Boko Haram da hukuma ke nema ruwa a jallo, don shine na lamba 176 a jerin sunaye. Dayake jawabi sadda aka kama shi, Nafiu yace “Na kashe sama da mutane 150 a karamar hukumar Baga na jihar Borno kadai.” Sai dai ya nemi al’umma da su mai aikin gafara.

A wani labarin kuma, Sama da ‘yan Boko Haram 200 ne suka far ma wata bataliyan sojojin Najeriya a harin ba zata inda suka kashe sojoji 8 sannan suka raunata wadansu 11. Sojin Najeriya sun yi arangama da Boko Haram din a batakashin da ya dauki kusan awa daya ana gwabzawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli barnar da Boko Haram tayi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel