Wani matashi dan shekara 23 ya kashe kansa a Adamawa

Wani matashi dan shekara 23 ya kashe kansa a Adamawa

- Majiyar mu ta rawaito mana cewa kamin matashin mai suna Musa Fedelis ya kashe kansa sai da ya daki mahaifiyarsa sannan karya mata a kafa

- Domin ja masa kunne da ta yi a kan wasu munanan ayyukan da yake tabkawa

Bayan gama hatsaniya da mahaifiyar tasa ne, da ya ga yan uwansa sun shigo gidan sun yi gaba da mahaifiya tasu ne, sai ya fada dakinsa ya kulle, inda su kuma suka yi banza da shi.

Sai da suka ji shirun ya yi yawa sannan suka bude dakin nasa da karfin tsiya inda suka gan shi rataye a rufin dakin nasa.

Wani daga cikin yan uwan nasa ya zargin mamacin da shan giya kamin aikata lamarin.

Wani matashi dan shekara 23 ya kashe kansa a Adamawa

Wani matashi dan shekara 23 ya kashe kansa a Adamawa

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa ya gana da magajin Babachir

NAIJ.com ta samu labarin wata yayar mamacin ta kuma bayyana cewa ba a dade ba wata mata ta shigo gidan tare da ciki, inda ta zayyana cewa cikin na wanda ya aikata kisan kan nasa ne.

Sai dai mai magana da yawun Rundunar Yan-sandan jihar Adamawa Othman Abubakar , ya ce ya ji labarin faruwar lamarin, amma babu wani rahoto da ya zo masu a hukumance kamin hada rahoton.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma tambaya akeyi ko me yasa muatane ke kashe kansu?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel