EFCC: Jami'an mu basu kai wani samame ba a gidan Sanata Danjuma Goje

EFCC: Jami'an mu basu kai wani samame ba a gidan Sanata Danjuma Goje

- Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annadi watau EFCC karkashin shugabancin Ibrahim Magu ta karyata rade-raden dake yawo cewa sun kai samame a gidan Sanata Mohammed Danjuma Goje.

- Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta na Tuwita inda tace bata da masaniya ko kadan a hakan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sannan kuma sai hukumar ta shawarci mutane su yi facali da dukkan labaran da ke nuni da cewa wani abu mai kama da hakan ya faru.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a jiya wasu majiyoyi sun ruwaito cewa a Najeriya jami'an tsaro sun kai same gidan tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje.

Sanata Goje ya tabbatar wa wasu majiyiyi cewa binciken da jami'an 'yan sanda ke yi daki-daki a gidansa dake unguwar Asokoro, a babban birnin tarayyar kasar, Abuja, da yammacin Alhamis.

EFCC: Jami'an mu basu kai wani samame ba a gidan Sanata Danjuma Goje

EFCC: Jami'an mu basu kai wani samame ba a gidan Sanata Danjuma Goje

KU KARANTA: Darajar Naira na ci gaba da tashi a kasuwa

Sanata Goje mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya ce bai san dalilin binciken ba, kuma ba a bashi takardar sammaci ba gabanin binciken.

Danjuma Goje ya mulki jihar Gombe tsawon shekar takwas.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wani tsagera ne a Kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel