Majalisar dattijan Najeriya ka iya mayar da Ndume – Bukola Saraki

Majalisar dattijan Najeriya ka iya mayar da Ndume – Bukola Saraki

- Sanata Bukola Saraki ya ce ana gudanar da tuntuba a bayan fage don ganin an janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume

- A cewar Bukola Saraki ya yi yakini akwai abin da zai faru idan majalisar ta koma aiki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya ce ana gudanar da tuntuba a bayan fage don ganin an janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume.

A cewar Bukola Saraki ya yi yakini akwai abin da zai faru idan majalisar ta koma aiki.

"Na tabbata za a ci gaba da tattaunawa idan muka koma zaure majalisa, abu ne da kowa zai so ya ga an daidaita."

Majalisar dattijan Najeriya ka iya mayar da Ndume – Bukola Saraki

Bukola Saraki ya ce ana gudanar da tuntuba a bayan fage don ganin an janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume

NAIJ.com ta tuna cewa a karshen watan Maris ne Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da Ndume wanda tsohon shugaban masu rinjaye ne sakamakon kiran da ya yi don a binciki zargin da ake yi wa shugaban majalisar da kuma Sanata Dino Melaye.

Sai dai bayan kammala bincike, sai kwamitin da'a na majalisar ya wanke Bukola Saraki daga zargin shiga da mota kasar ba bisa ka'ida ba, da kuma Dino Melaye kan amfani da takardar shaidar digiri na bogi.

KU KARANTA KUMA: Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi – Fadar shugaban kasa

Sanata Ali Ndume ya dade yana takun-saka da shugaban majalisar, Bukola Saraki amma abin ya fito fili lokacin da aka sauke shi daga mukamin shugaban masu rinjaye.

Ya ce zargin cewa saboda abin ya shafe shi ne aka dakatar da Ali Ndume, duk ba haka ba ne, magana ce da kwamitin da'a ya gudanar da bincike a kanta.

Bukola Saraki ya ce a matsayinsa na shugaban majalisa ba shi da ikon daukar wani mataki a kan wani ɗan majalisa don kawai, yana jin an tsane shi.

A cewarsa tsarin dimokradiyya zai karfafa ne idan ana bin ƙa'ida ko da kuwa wani tsari bai yi wa mutum dadi ba.

Ya ce sanata Ndume ya san hanyoyi gabatar da korafe- korafe irin wadannan, ba tare da an tozarta majalisa ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun koka tare da rokon karda a rushe masu gidajen su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel