An nada sababbin SGF da shugaban NIA na rikon kwarya

An nada sababbin SGF da shugaban NIA na rikon kwarya

– Shekaran jiya Shugaban kasa ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya

– Shugaba Buhari ya bayyana cewa za ayi bincike game da su Babachir David Lawal

– Yanzu haka har mukaddashiyar Sakataren ta soma aiki

An nada sababbin SGF da shugaban NIA na rikon kwarya

An nada sabon SGF na rikon kwarya

Idan ana tare da NAIJ.com dai a shekaran jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal bisa wasu zargi na bada kwangiloli ba tare da ka’ida ba.

Yanzu haka kuna da labari cewa har Dr. Lawal Habiba ta maye gurbin na sa zuwa lokacin da za a kammala bincike nan da makonni biyu. Dama dai shugaban kasar ya bada umarni babban Sakataren din-din-din a Ofishin ya ja ragamar aikin.

KU KARANTA: Yadda aka yi da shugaban NIA bayan an dakatar da shi

An nada sababbin SGF da shugaban NIA na rikon kwarya

Osinbajo ya gana da sababbin SGF da shugaban NIA

A jiya mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Dr. Habiba Lawal wanda za ta maye gurbin na SGF. Osinbajo ya kuma gana da Sufeta Janar na ‘Yan Sanda da shugaban DSS da sauran manyan Jami’ai har Gwamnan Adamawa Jibrila Bindow dai ya kai ziyara Fadar.

Haka kuma Osinbajo ya tattauna da shugaban Hukumar NIA na rikon kwarya Ambasada Arab Yadam. Haka zalika idan ba a manta ba an dakatar da shugaban Hukumar NIA mai leken asiri Ambasada Ayodele Oke bayan EFCC ta bankado wasu makudan miliyoyin daloli a Legas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

APC na cikin matsala inji wani babban dan Jam'iyyar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel