Naira na cigba da kara daraja a kasuwa

Naira na cigba da kara daraja a kasuwa

– Farashin Naira na cigaba da dagawa a kasuwa yanzu

– Dalar Amurka na cigaba da yin kasa a kasuwar canji

– Bankin kasar na CBN na cigaba da sa hannu

Naira na cigba da kara daraja a kasuwa

Gwamnan babban bankin CBN

Jiya NAIJ.com ta kawo labari cewa darajar Dalar Amurka na yin kasa a wannan makon. Dama Shugaban ‘Yan canji watau BDC na Najeriya Alhaji Aminu Gwadabe ya bayyana cewa dalar za ta sauko kwanan nan.

A da can Dalar Amurkar ta kara komawa kimanin N400 wanda yanzu ta sauko har zuwa N385 a kan kowace Dala guda. Haka kuma farashin EURO ya koma N410 yayin da Pound Sterling na kasar Ingila ya koma N495.

KU KARANTA: Naira ta kara daraja a kasuwa

Naira na cigba da kara daraja a kasuwa

Naira na kara daraja a hannun yan canji

Har ya zuwa Ranar Talata kuwa kuwa farashin EURO yana kan N430 yayin da Pound na Ingila yake N497. An dai samu canji matuka a kasuwa da kuma bankunan kasar bayan kokarin da CBN ta cigaba da yi na sakin makudan daloli domin darajar dalar ta sauko.

‘Yan kasuwa sun yi kira a rika sakin kudin da Hukumar EFCC ta bankado zuwa cikin kasuwar domin abubuwa su kara rangwame. Babban bankin kasar na CBN ya saki sama da Dala Miliyan 200 wannan makon cikin kasuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Buhari ya fitar da Najeriya cikin matsin tattali

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel