Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

– Shugaba Buhari ya dakatar da Babachir David Lawal daga matsayin Sakataren Gwamnati

– Akwai yiwuwar Shugaba Buhari ya nemi wanda zai maye gurbin sa

– Ana zargin Sakataren Gwamnatin Kasar da wasu laifuffuka

Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

Shugaba Buhari na neman sabon Sakataren Gwamnati?

Dama tun karshen bara akwai kishin-kishin din cewa Shugaba Buhari na neman sabon Sakataren Gwamnati bayan da zargin da ke kan Mr. Babachir Lawal su ka yi nauyi inda Majalisar Dattawa ta jefawa Mista Babachir din kashi dumu-dumu a jika.

Daga cikin wadanda ake tunanin za su iya maye gurbin Babachir din idan har karshen sa ya zo akwai:

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada sababbin mukamai

Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

Watakila a nada Oshiomole ya maye gurbin Babachir

1. Adams Oshiomole

Tsohon Gwamnan Jihar Edo na da alaka mai kyau da shugaban kasa da kuma Jam’iyyar APC. Yanzu haka ana ta kira a nemi wani matsayi a ba tsohon Gwamnan.

2. Audu Ogbeh

Cikin wadanda ake sa rai su canji Sakataren Gwamnatin, akwai Audu Ogbeh wanda shine Ministan noma na Kasar.

Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

Shugaba Buhari ya dakatar da Babachir

3. Sauran Ma’aikatan Gwamnati

Akwai kuma wasu tsofaffin Ma’aikatan Gwamnati da ake tuntuba domin su canji Babachir din. Yanzu haka dai Dr. Lawal Habiba ta maye gurbin na sa zuwa lokacin da za a kammala bincike nan da makonni biyu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tattalin arziki: Shin Buhari na aiki kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel