An kai samame gidan Sanata Danjuma Goje a Abuja

An kai samame gidan Sanata Danjuma Goje a Abuja

- Jami’an hukumar EFCC sum mamaye gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje dake Abuja a yammacin ranar Alhamis

- Hukumar EFCC ta sanar da cewa ba ita bace ta aika da jami’an ta gidan Goje, Umarni ne daga sifeton rundunar ‘yan sandan kasa Idris Ibrahim ga jami’an sa da su je gidan domin gudanar da bincike

Rahotanni dake zuwa ma NAIJ.com shine cewan jami’an hukumar EFCC sum mamaye gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje dake Abuja a yammacin ranar Alhamis.

Jami’an ‘yan sanda 25 ne da wadansu sanye da fararen kaya suka kai farmakin gidan tsohon gwamnan.

Hukumar EFCC ta sanar da cewa ba ita bace ta aika da jami’an ta gidan Goje, Umarni ne daga sifeton rundunar ‘yan sandan kasa Idris Ibrahim ga jami’an sa da su je gidan domin gudanar da bincike.

An kai samame gidan Sanata Danjuma Goje a Abuja

Jami'an EFCC kai samame gidan Sanata Danjuma Goje a Abuja

Bayanan da aka samu akan wannan samame da aka kai gidan Goje yana da nasaba ne da bayanai da aka samu cewa akwai wasu miliyoyin kudade da aka boye a gidan na sa.

KU KARANTA KUMA: Mutane 3 da Buhari zai iya nadawa su maye gurbin Babachir

A halin yanzu, bayan dakatar da babban sakataren gwamnati, Babachir Lawal da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu, babban sakatariya ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) Dr. Habibat Lawan, ta fara gudanar da aiki a matsayin mukaddashin gwamnatin tarayya.

An zargi Babachir da aiakata rashawa a kwangilar yunkurin fadar shugaban kasa a kan yan Arewa maso Gabas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jami'in APC ya bayyana kalubalen da jam'iyyar ka iya fuskanta a 2019.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel