Dalilin da ya sa ba za mu saki El-Zakzaky ba – VP Osinbajo

Dalilin da ya sa ba za mu saki El-Zakzaky ba – VP Osinbajo

-Osinbajo yace gwamnati ba zata saki Ibrahim El-Zakzaky ba

-Kana kuma gwamnati ta daukaka kara kotun Afil kan hukuncin da aka bayar

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi fashin baki game da kace-nacen da akeyi da zanga-zanga akan rashin bin umurnin kotu wajen sakin shugaban mabiya addinin Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky.

A wata jawabin bidiyo da aka wallafa a shafin ra’ayi da sadan zumuntan Tuwita na gwamnati, Osinbajo ya ce shi mutum ne da ke tsayawa tsayin daka wajen ganin an mutunta umarnin kotu.

Ya bayyana cewa dalilin da ya sa gwamnati ba za ta saki shugaban kungiyar mabiya addini Shi'a Ibrahim El-Zakzaky ba, shi ne saboda ta daukaka kara kan hukuncin kotun da ya bada daman a sake shi.

Dalilin da ya sa ba za mu saki El-Zakzaky ba – VP Osinbajo

Dalilin da ya sa ba za mu saki El-Zakzaky ba – VP Osinbajo

Gwamnatin shugaba Buhari na shan suka iri-iri kan rashin sakin El-Zakzaky, da shugaban masu yakin neman Biafra Nnamdi Kanu da kuma tsahon mai ba da shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki.

Mista Osinbajo ya ce : "Duk lokacin da kotu ta ba da wani umarni, to ya zama dole a yi aiki da shi.Sai dai kuma muna da damar da za mu daukaka kara,".

KU KARANTA: El-Rufai ya bada umurnin damke wani dan jarida

A watan Disamban 2016 ne kotu ta yanke hukuncin cewa a saki El-Zakzaky ta saba cikin kwana 45.

An kama shi ne a watan Disambar shekarar 2015, bayan wani rikici da sojoji suka yi da mambobin kungiyarsa a Zariya, inda aka kashe daruruwan mabiyansa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel