Dalilin da yasa banyi magana lokacin rikicin Ile-ife ba – Sarki Sanusi

Dalilin da yasa banyi magana lokacin rikicin Ile-ife ba – Sarki Sanusi

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya kai ziyara fadar Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi da ke Ile-ife, jihar Osun.

Yayinda sarkin Kano ke magana a jiya Laraba inda ya ai ziyara wajen da akayi rikici tsakanin kabilar Hausawa da Yarbawa a Sabo, yace shi da sarkin Musulmai sun ki magana akan al’amarin ne saboda maganar da Oba Ogunwusi yayi akan rikicin ta isar.

Ya yabawa Ooni of Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, akan rawar da ya taka ta hanyar daukan alhakin abinda ya faru da kuma kula da kowa a garin ba tare da bambancin yare ko addini ba.

Dalilin da yasa banyi magana lokacin rikicin Ile-ife ba – Sarki Sanusi

Sarki Sanusi da Ooni of Ife

Yace : “ Ziyarar da na kawo yau na farin ciki ne kuma na bacin rai. Na farin ciki ne saboda damace na tayaka murnan hawa mulkinka, kuma na bacin rai ne saboda tanada alaka da rikicin Ile-Ilfe da akayi kwanakin baya.”

“Na san jama’a ta a arewa suna koka min akan al’amarin amma nayi shiru akai. Bari in bayyana cewa lokacin da wannan abu ya faru, Ooni of Ife ya kirani da sarkin Musulmi; kuma mu ma mun kira lokuta da dama kuma mun gamsu da yadda ya kula da al’amarin.”

KU KARANTA: An damke mutane 53 da suka halarci auren jinsi a jihar Kaduna

“Mun ga rawan da ya taka wajen bayyana cewa shine uban kowa a kasar Yoruba, ba tare da banbancin yare ko addini ba, kuma mukayi tunanin cewa tunda Ooni na iyakan kokarinshi na kwantar da tarzoman, babu bukatan waninmu ya zo yayi wata maganan da zai iya tayar da kura ba.”

“Bari in bayyana cewa ni da sarkin musulmai ya kasance muna nan a yau amma sultan yayi tafiya sai yace in wakilcesa da dukkan sarakunan arewa.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel