Fayose ya kai hari ga shugaba Buhari bayan dakatar da sakataren gwamnati, da shugaban NIA

Fayose ya kai hari ga shugaba Buhari bayan dakatar da sakataren gwamnati, da shugaban NIA

- Gwamna Ayo Fayose ya bayyana dakatar da Babachir Lawal da Buhari yayi a matsayin rufa-rufa

- Gwamnan ya ce shugaban kasa na kokarin yin rufa-rufa ne a kan rashawa

-Ya zargi shi da tsare mambobin jam’iyyar APC

Gwamna Ayodele Fayose na Ekiti ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan ya dakatar da babban sakataren gwmanatin tarayya, Babachir Lawal da kuma darakta janar na hukumar leken asiri, Ayodele Oke.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

Shugaban kasa ya dakatar da jami’an biyu ne bisa ga al’amarin da ya shafi rashawa a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu amma Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin rufa-rufa.

A cikin wata sanarwa daga hannun mataimakin sa a kafofin watsa labarai, Lere Olayinka, Fayose yace kafa wata kwamiti domin tayi bincike cikin al’amarin jami’an guda biyu rufa-rufa ne da ya hada da fadar shugaban kasa.

Ya ce: “Shin shugaban kasa zai kafa wata kungiyar bincike idan da ace wannan zambar na da alaka da wani a jam’iyyar PDP ko kuma yan jam’iyyar sa da basu da kyakkyawar alaka?

“Bayan haka, meye ruwan kwamitin shugaban kasa da binciken laifi? Shin suna fada ma yan Najeriya cewan basu yarda da dukkan hukumomin bincike na gwamnati bane wanda suka hada da hukumar EFCC da DSS?

KU KARANTA KUMA: Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

"Gwamnatin Buhari na aiki kamar akwai gwamnatoci da dama a cikin gwamnati daya. Da alama akwai shugabanni da yawa a cikin fadar shugaban kasa kuma wannan ne dalilin rudani a ko ina."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Iyalan matar da aka harbe bisa kuskure sun nemi a bi masu hakkin su:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel