Shekaru 3 da sace ýan matan Chibok: Muhimman abubuwa 7 dangane da ýan matan

Shekaru 3 da sace ýan matan Chibok: Muhimman abubuwa 7 dangane da ýan matan

- Yan matan Chibok sun cika shekar 3 cif cif a hannun kungiyar Boko Haram

- Zuwa yanzu akwa sauran yan mata 195 a hannun kungiyar Boko Haram

A satin daya gabata ne yan matan chibok din da kungiyar ta’addanci na Boko ta sace su suka cika shekaru 3 a inda babu wanda ya sani sai Allah.

Ganin haka ya sanya NAIJ.com kawo muku rahoton wasu muhimman abubuwa guda 7 game da yan matan da masu karato baus sani ba, ko kuma suka manta.

1- A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sace yan matan makarantar mata dake garin Chibok su 276 a jihar Borno.

KU KARANTA: Munyi da na sanin zaben shugaba Buhari – Iyayen yan matan Chibok

2- Yan mata 81 daga cikinsu ne suka gudo daga hannun mayakan Boko Haram daga dajin Sambisa, yayin da wasu kuma tun a hanya suka tsere

Shekaru 3 da sace ýan matan Chibok: Muhimman abubuwa 7 dangane da ýan matan

Wasu cikin iyayen ýan matan Chibok

3- A shekarar data gabata ne Boko Haram ta sako yan mata 21 daga cikin yan matan Chibok din biyo bayan tattaunawa tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya.

4- Sakamakon damuwa da sace yan matan, iyayen su maza da mata su 19 sun kamu da cututtuka daban daban sanadiyyar bakin cikin rashin dowawar yayan nasu, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar dukkanin su, su 19.

Shekaru 3 da sace ýan matan Chibok: Muhimman abubuwa 7 dangane da ýan matan

Yan matan Chibok da suka tsira

5- Zuwa yanzu akwai yan matan Chibok su 195 da suka rage a hannun yan ta’addan Boko Haram, kuma har yanzu ba’a tabbatar da halin da suke ciki ba.

6- A watan Agustan shekarar 2014 ne Boko Haram ta saki wani bidiyo dake nuna yan matan Chibok sanye da hijabai suna karatun Qur’ani, inda ma daya daga cikinsu tayi bayani da yaren kanuri.

7- A watan Mayun 2016 ne Sojoji suka gano wata daga cikin yan matan mai suna Amina Ali wanda ta bayyana ma iyayenta cewar ba’a basu a binci, kuma wasu daga cikin yan matan sun mutu sakamakon halin da suke ciki.

Alhinin tunawa da yan mata Chibok bayan shekaru 3

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel