YANZU YANZU: El-Rufai ya ba da umurnin kama wani dan jarida

YANZU YANZU: El-Rufai ya ba da umurnin kama wani dan jarida

- An kama shi ne sakamakon wallafa wani rahoto wanda ake ganin suka ne ga gwamnatin jihar.

- Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ba da umurnin kama wani dan jarida a jihar

- Dan jaridar ya zamo na shidda kenan da Gwamna El-Rufai ya kama tunda ya hau kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu na 2015

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya ba da umurnin kama Mista Midat Joseph, wani mai kawo ma jaridar Leadership rahoto.

Jami’an tsaro ne suka kama shi a gidan sa a safiyar ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu.

A cewar majiyoyi, dan jaridar wanda ke tsare a yanzu haka a Kaduna ya wallafa wani rahoto wanda ake ganin suka ne ga gwamnatin jihar.

YANZU YANZU: El-Rufai ya ba da umurnin kama wani dan jarida

An zargi El-Rufai ya ba da umurnin kama wani dan jarida

NAIJ.com ta tattaro cewa Midat ya zamo dan jarida na shidda kenan da Gwamna El-Rufai ya kama tunda ya hau kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu na 2015.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

A halin da ake ciki, kwanaki sanata Shehu Sani ya sanya ma El-Rufai zafi, kan jawabinda ya yi game da shugaban jam’iyyar APC ta kasa Asiwaju Bola Tinubu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan wani dan Najeriya da yayi korafi a kan ayyukan shugabannin Najeriya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel