Darajan Naira yayi tashin gauron zabi a kasuwannin bayan fagge

Darajan Naira yayi tashin gauron zabi a kasuwannin bayan fagge

- Darajan Naira ya farfado daga faduwar da yayi a kimanin sati biyu da suka gabata

- A yau ana siyar da dalan Amurka guda akan N395

A tsakanin kwanaki biyu babban bankin Najeriya, CBN ta afka dala miliyan 380 a kasuwan canji, wanda hakan yayi sanadiyyar rugujewar darajan dala.

A ranar Talata 18 ga watan Afrilu ne bankin ta zuba $280m, inda a ranar Laraba 19 ga watan Afrilu ta sake zuba $100m duk a kasuwar canji wanda ta baiwa yan canji da zasu siyar ma mabukata a kwanaki 7

KU KARANTA: An bayyana dalilin da ya sa farashin Dala ke yin tashin gwaron zabo (Karanta)

Kaakakin Bankin, Okorafor yace bankin ta lura cewar bankunan yan kasuwa na samar da isashen dala ga abokan cinikayyarsu, sa’annan ya kara da cewa a ranar Alhamis babban banki zata cigaba da siyar da dala 20,000 ga kananan yan canji.

Darajan Naira yayi tashin gauron zabi a kasuwannin bayan fagge

Canjin Naira da Dala

Okorafor yayi ma yan kasuwa albishir inda yace dala na cigaba da samun daraja, kuma darajarta zai daure saboda CBN zata cigaba da zuba makudan daloli a kasuwar canjin kudi. Daga karshe ya jaddada burin CBN na ganin ta samar da isashshen dala ga mabukata.

A yau Alhamis 20 ga watan Afrilu ana siyar da dala akan N395, inda ake siya akan N385, sai kudin kasar ingila wato pan, akan N495, inda ake siya akan N485. Shima Euro ana siyar da shi akan N425 a siya N410, kamar yadda NAIJ.com ta tattaro bayanai.

A wani labarin kuma bankin duniya ya yaba ma hanyoyin da babban bankin Najeriya ke bi na kara yawan daloli a kasuwar canji don samar ma Naira daraja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tashin farashin dala, kalli farashin kayan abinci a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel