Sabon ango ya hallaka wani mai kokarin yima amaryarsa fyade

Sabon ango ya hallaka wani mai kokarin yima amaryarsa fyade

- Sabon ango ya hallaka wani da yayi kokarin shiga gonarsa

- Kakakin hukumar yansanda SP Abdul Jinjiri,ya tabbatar da hakan

Hukumar yan sandan jihar Jigawa ta damke wani Dahiru Adamu, dan kauyen Agufa a karamar hukumar Miga da laifin kisan wani Ishaq Said, wanda yayi silale cikin gidansa domin yiwa amaryarsa fyade.

Adamu ya far ma Isyaku ne bayan ya zo karo na 4 cikin kwanaki 4 domin yiwa matarsa fyade.

Sabon ango ya hallaka wani mai kokarin yima amaryarsa fyade

Sabon ango ya hallaka wani mai kokarin yima amaryarsa fyade

Kakakin hukumar yan sanda jihar, SP Abdul Jinjiri, ya bayyanawa jaridar Daily Trust yace Adamu ya makawa Isyaku gora akai ne wanda yayi sanadiyar mutuwarsa.

KU KARANTA: Dalilin da yasa aka dakatad da SGF David Lawal

Ya kara da cewa Adamu na ofishin yan sanda yanzu ana gudanar da bincike.

Adamu yace: “Lokacin da ya zo karo na hudu domin tabbatar da cewa yayiwa matana fyade, sai na kai masa hari da sanda. Na buga masa sau 2 a bayansa kuma sau daya a kafa.”

https://facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel