Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

- Mataimakin shugaban kasa ya gana da iyayen yan matan Chibok

- Ganawar tasu ta wakana ne a ofishinsa dake fadar shugaban kasa

A Laraba 19, ga watan Afrilu ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu ganawa da wasu daga cikin iyayen yan matan Chibok.

Iyayen sun kawo ma mataimakin shugaban ziyarar ne don alhinin cika shekaru 3 da sace yan matan na Chibok, inda suka samu zantawa da shi a kan batun ceto yan matan tare da nuna masa damuwarsu game da hakan.

KU KARANTA: Rundunar Soji ta kai harin samame akan yan ta’addan Boko Haram (Hotuna)

Mataimakin shugaban kasa ya tabbatar ma iyayen yaran cewar gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na ganin an dawo da sauran yan matan gida cikin koshin lafiya.

Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

Osinbajo tare da iyayen ýan matan Chibok

A satin daya gabata ne NAIJ.com ta kawo muku rahoton cika shekaru 3 da sace yan matan makarantar kwana dake garin Chibok na jihar Borno da aka sace su tun a watan 2014 yayin da suke zana jarabawar WAEC.

Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

Osinbajo yayin ganawa da iyayen ýan matan Chibok

Zuwa yanzu dai 81 da daya sun dawo, ciki har da wadanda suka tsere daga hannun yan ta'addan da kuma wadanda kungiyar ta sako su sakamakon tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

Osinbajo tare da iyayen ýan matan Chibok

Osinbajo ya karɓi bakoncin iyayen ýan matan Chibok

Zaman Osinbajo da iyayen ýan matan Chibok

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Alhinin shekaru 3 da sace yan matan Chibok

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel