Yan sanda su kama rikakken kwamandan kungiyar Boko Haram a Bauchi

Yan sanda su kama rikakken kwamandan kungiyar Boko Haram a Bauchi

- Rundunar yan sandan Najeriya, sashin Baushi, ta kama wani rikakken kwamandan kungiyar Boko Haram

- An bayyana wanda ake zargin a matsayin Muhammad Adamu Nafiu mai shekaru 25

- An rahoto cewa Nafiu ya yi ikirarin kashe sama da mutane 150 a karamar hukumar Baga , jihar Borno

Rundunar yan sandan Najeriya, sashin Bauchi, ta sanar da kamun wani kwamandan kungiyar Boko Haram mai shekaru 25 mai suna Muhammad Adamu Nafiu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, Garba Baba Umar, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu, yace Nafiu ya kasance rikakken shugaba a kungiyar Boko Haram, wanda ya gudu daga dajin Sambisa bayan hukumar sojin Najeriya sun kwato.

KU KARANTA KUMA: Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

Nafiu, wanda ya kasance dan asalin Balanga, jihar Gombe, ya koma kauyen Tama, inda manyan jami’an doka suka kama shi a ranar 12 ga watan Afrilu.

Yan sanda su kama rikakken kwamandan kungiyar Boko Haram a Bauchi

Nafiu ya yi ikirarin cewa ya kashe sama da mutane 150 a karamar hukumar Baga na jihar Borno

An karanta sanarwan kamar haka: “Binciken farko ya bayyana cewa wanda ake zargin na cikin wadanda hukumar soji ke nema ruwa a jallo dauke da lamba 176 a cikin jerin sunayen ta, jaridar Sun ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar AdamawaHukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

“Ya yi ikirarin cewa ya kashe sama da mutane 150 a karamar hukumar Baga na jihar Borno kadai.

“Al’amarin na karkashin bincike wanda daga nan ne za’a mika mai laifin zuwa ga hukumar da ta dace."

A halin da ake ciki, a ranar Talata, 18 ga watan Afrilu NAIJ.com ta samu labarin cewa rundunar bataliya 26 ta harbe yan ta’addan Boko Haram guda shidda.

An kashe yan ta’addan ne a wani aiki da sojin Operation Lafiya Dole suka gudanar a mafakar yan ta’addan a Dissa da kuma yankin Patawe dake jihar Borno.

Daraktan bayanai na hukumar Sani Usman a cikin wata sanarwa ya ce yan ta’adda da dama sun samu rauni a lokacin harin.

Usman yace an samo kayayyaki da dama daga yan ta’addan ciki harda bindigan AK-47.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon wata yarinya da ta tsira daga rikicin Boko Haram.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel