Kasar Rasha ta miƙa ma Najeriya katafaren jiragen yaƙi guda 2

Kasar Rasha ta miƙa ma Najeriya katafaren jiragen yaƙi guda 2

- Rundunar sojin sama na Najeriya ta karbin sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha

- Rundunar tace jiragen zasu kara mata karin gwiwa a yaki da ta'addanci

Rahotannin sun watsu na cewar kasar Rasha ta aiko da wasu manyan jiragen sama na yaki ga rundunar sojin saman Najeriya.

Daraktan ayyuka na rundunar mayakan sojin sama Air Vice-Marshal Adebayo Amao ne ya bayyana haka a wani taro daya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai da Buratai sun ƙaddamar da ‘Operation Harbin Kunama II’ a kudancin Kaduna

Amao ya tabbatar ma mahalarta taron cewa jiragen yakin zasu kara musu kaimi wajen yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram tare da basu nasara gwaggwaba akan su, musamman a kokarinsu na kakkabe su daga yankin Arewa maso gabas.

Kasar Rasha ta miƙa ma Najeriya katafaren jiragen yaƙi guda 2

Samfurin jirgin yaƙi

Amao ya kara da cewa: “Nan bada dadewa bane kasar Rasha zata sake aiko mana da ire iren jiragen nan, sa’annan muma zamu aika da matuka jirgin zuwa yankin Arewa maso gabas da sauran yankunan kasar nan inda ake rikici.”

Kasar Rasha ta miƙa ma Najeriya katafaren jiragen yaƙi guda 2

Samfurin jirgin yakin

Daga karshe NAIJ.com ta jiyo Amao yana fadin rundunar mayakan sojin sama ta fadada inda take gudanar da ayyukanta daga Arewa maso gabas zuwa sauran yankunan kasar, inda yace sun kusan cimma bukatarsu a Arewa maso gabas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jirgin yakin Najeriya na cigaba da zubar wuta a kan Boko Haram, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel