Dalilin da yasa aka dakatad da SGF Babachir David Lawal

Dalilin da yasa aka dakatad da SGF Babachir David Lawal

- An dakatad da SGF Injiniya Babachir Davida Lawal, kuma ya bar kujerarsa

-Kana kuma an sallami shugaban hukumar NIA, Olu Oke, a lokaci daya

A jiya ne Laraba, 19 ga watan Afrilu 2017, mai magana da yawun shugaban kasa, Mr. Femi Adesina, ya alanta a wata jawabin da ya saki a shafinsa na Fezbukcewa shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da sakataren gwamnatin tarayya, Injiniya Babachir David da kuma shugaban hukumar leken asirin tarayya, Olu Oke.

Wannan sanarwa na daga cikin abun da ya farantawa yan Najeriya rai bisa ga tuhumce-tuhumcen da akeyiwa Babachir David.

Adesina ya bayyana cewa dalilin da yasa aka dakatad da su shine domin samun gudanar da bincike a cikin al’amura guda biyu da ake zargin su da shi.

Dalilin da yasa aka dakatad da SGF Babachir David Lawal

Dalilin da yasa aka dakatad da SGF Babachir David Lawal

Shugaba Buhari ya nada wata kwamitin bincike karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da kuma mambobi wanda ya kunshi ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, da kuma mai baiwa Buhari shawara kan tsaro, Babagana Munguno.

Mai magana da yawun shugaban kasa yace ana bukatan kwamitin su kawo sakamakon bincikensu cikin kwanaki 14.

KU KARANTA: Naira ta kara daraja a kasuwan canji

Ana tuhumar Babachir da bada kwagilan miliyoyi ga kamfanoninsa wanda ya kunshi bada miliyan12 domin cire ciyawa a sansanin yan gudun hijra.

Shi kume Oke rikicin shi ta fara ne bayan hukumar EFCC ta gani kudi a gidan Ikoyi kuma yace ai kudinsu ne wanda tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya basu.

A yanzu dai Babachir David Lawal ya bar fadar shugaban kasa kuma ba zai dawo bas a shugaba Buhari ya bukaci ganinsa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel