Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri (HOTUNA)

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri (HOTUNA)

- Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri

- Hukumar ta kaddamar da aikin ne a matsayin gudunmawar ta a cikin kokarin da akeyi na ganin an rage yaduwar cutar ta daji a duniya baki daya

- Mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Usman Mamman Surkwa ya yi godiya ga hukumar sojin Najeriya da ta zabi gina cibiyar tantance cutar ta daji a Maiduguri

A jiya ne mai bada shawara a kan al’amarin tsaro na kasa, Manjo Janar Mohammed Mongunu ya kaddamar da cibiyar tantance cutar daji na farko a jihar Borno a sansanin hukumar sojin Najeriya dake Maiduguri.

Da yake magana a gurin taron mai bada shawara a kan al’amarin tsaro na kasa yace hukumar ta kaddamar da aikin ne a matsayin gudunmawar ta a cikin kokarin da akeyi na ganin an rage yaduwar cutar ta daji a duniya baki daya.

Yace: Abune mai ban sha’awa da kuma son ganin cewa hukumar sojin Najeriya ta yi jagora a Najeriya a gangamin da akeyi kan wadannan muggan cututtuka.”

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri.

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri.

A nashi jawabin, mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Usman Mamman Surkwa ya yi godiya ga hukumar sojin Najeriya da ta zabi gina cibiyar tantance cutar ta daji a Maiduguri tare da bayyana cewa himmar zai taimaka gurin rage kalubalen dake kewaye da cutar aji a jihar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar AdamawaHukumar NSCDC ta kama dan Boko Haram a jihar Adamawa

A nashi bangaren, shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Baba Abubakar ya bayyana cewa cibiyar zata kula da sojoji da yan fararen hula a jihar. Ya kara da cewa kayayyakin da aka zuba a cibiyar zasu taimaka sosai gurin gane cutar daji a matakin farko sannan kuma aba da kulawar da ya kamata a lokacin da aka gano cutar domin ceto rayuka.

NAIJ.com ta tattaro maku sauran hotuna daga taron:

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri.

shugaban hukumar a lokacin da yake jawabi a gurin taron

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri.

Lokacin da ake kaddamar da bude cibiyar

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a Maiduguri.

Hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tantance cutar daji a jihar Borno

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yadda hukumar soji ta yaki yan ta'addan Boko Haram:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel