Madalla: Naira na kara daraja a kasuwa

Madalla: Naira na kara daraja a kasuwa

– Farashin Dalar Amurka na dan yi kasa

– Naira kuma ta fara mikewa a kasuwar canji

– CBN na cigaba da zazzago daloli a kasuwa

Madalla: Naira na kara daraja a kasuwa

Madalla: Naira na kara daraja a kasuwa

NAIJ.com na da labari cewa darajar Dalar Amurka na dan yi kasa a wannan makon. Dama Shugaban ‘Yan canji watau BDC na Najeriya Alhaji Aminu Gwadabe ya bayyana cewa dalar za ta sauko wannan makon.

Babban bankin kasar na CBN na cigaba da sakin makudan daloli domin darajar dalar ta sauko kasa. A kwanakin nan kuwa Dalar ta sauko kadan inda farashin EURO yake kan N430 yayin da Pound na Ingila ya koma N497.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya raba buhunan shinkafa ga yan gudun hijira

Madalla: Naira na kara daraja a kasuwa

Farashin Naira na kara dagawa

Naira dai ta kara darajar kadan ne bayan babban bankin kasar na CBN ya cigaba da sakin daloli ga bankuna da ‘Yan canji. Yanzu haka ma Bankin na CBN na shirin shigo da wani sabon tsari domin dalar ta yi sauki.

Jaridar World Economist da ke Landan tace Najeriya ta fito daga kangin matsin da ta samu na tattali haka kuma Hukumar tara bincike da alkaluman kasa watau NBS ta tabbatar da wannan rahoto. Hasashe na nuna cewa harkar kasuwanci yayi dagawar da bai taba yi ba tun bara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Chibok sun kai kukan su bayan shekaru 3

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel